31 Janairu 2026 - 08:14
Source: ABNA24
Iraq: Ta Tura Dakarun Hashdush Sha’abi Daga Basra Zuwa Kan Iyakar Iraki Da Siriya

Ofishin Rundunar Hashdush Sha’abi da ke lardin Basra ya sanar da aike da tawagar tallafin kayan aiki daga Basra zuwa kan iyakar Iraki da Siriya.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Ofishin Rundunar Hashdush Sha’abi da ke lardin Basra ya sanar a jiya, Juma'a, cewa tawagar tallafin kayan aiki ta shi daga Basra zuwa kan iyakar Iraki da Siriya.

A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Baratha, Birgediya Janar Fadel al-Basiri, darektan ofishin Rundunar Hashdush Sha’abi da ke Basra, ya sanar a cikin wata sanarwa cewa wannan ayarin kayan aiki a zahiri wani ayarin jama'a ne da aka aika don tallafawa da taimakawa jami'an tsaro da Rundunar Hashdush Sha’abi da ke zaune a kan iyakar Iraki da Siriya.

Ya kara da cewa: Aikewa da wannan ayarin yana nuna ruhin hadin kan kasa da kuma tsayawa tare da sojojin da ke kare tsaro da kwanciyar hankali na Iraki.

..........

Your Comment

You are replying to: .
captcha